Connect with us

Kiwon Lafiya

Jihohin Najeriya 16 sun nuna aniyar su ta shiga shirin ware wuraren kiwo ga makiyaya

Published

on

Jihohi goma sha shida cikin talatin da shida na kasar nan ne suka nuna aniyar su ta shiga cikin shirin nan na ware wuraren kiwo ga makiyaya mai taken: Cattle colonies.

Mai baiwa ministan noma da raya karkara shawara Dr. Olukayode Oyedele ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

Ya ce nan gaba ba da dadewa ba wasu karin jihohi za su nuna sha’awar su ta cin gajiyar shirin.

Dr. Olukayode Oyedele ya ce kowanne guda cikin cattle colonies da za a samar din zai kunshi wuraren kiwon dabbobi ashirin zuwa arba’in.

Haka zalika a cewar sa za a kuma samar da asibitocin dabbobi da kuma tsaro a yankunan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!