Labaran Wasanni
Kasar Mali ta lashe kofin Afurka ta matasa yan kasa da shekaru 20
Kasar Mali ta lashe kofin Afurka ta matasa ‘yan kasa da shekara 20 bayan da ta samu galaba Akan kasar Senegal da ci uku da biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Tun farko dai kasashen biyu sun tashi a wasa da ci daya da daya, wannan kuma wani ramuwar gayya ce da kasar ta Mali ta yi bayan tun farko Senengal din ta doketa da ci biyu da nema a wasan rukuni.
A wani ci gaban kuma, hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta amince da amfani da VAR a gasar cin kofin nahiyar Afrika da za a yi Bana a kasar Masar a watan Yuni zuwa watan Yuli.
Hukumar ta amince da amfani da na’urar ne jiya a jamhuriyar Niger bayan kammala gasar cin kofin Afrika na matasa ‘yan kasa da shekara 20, kuma wannan shine karo na farko a tarihin gasar cin kofin nahiyar Afrika da za a yi amfani da na’urar,
A wasan damben gargajiyar da ake yi a gidan wasa na Ado Bayero Square wasannin da aka kara a jiya,
Dan Sadauki da Arewa ya buge Autan Mai Takwasara Guramada.
Shagon Sojoji daga Arewa da Bahagon Kudu sun yi turmi biyu baba kisa.
Bahagon mai Takwasara ya buge Bahagon Onwando daga Arewa.
Shagon dan Bature daga Arewa ya kashe bahagon mai takwasara daga Guramada.