Connect with us

Labaran Wasanni

‘Yan wasan Najeriya sun kammala duk wani shiri domin tunkarar gasar cin kofin Afrika – Austin Eguavoen

Published

on

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Austin Eguavoen ya ce ya yi farin ciki da ‘yan wasan da ya gayyata 28 da za su fafata a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta AFCON a kasar  Cameroon.

Super Eagles dai za ta fafata da kasashen  Masar wato  (Egypt) da  Sudan da kuma  Guinea Bissau a rukunin da suke ciki na  D.

Gasar ta shekarar 2021 ta AFCON za ta gudana daga ranar 9 ga Janairu zuwa  6 ga Fabrairun shekarar 2022 a manyan biranen kasar Kamaru 5.

Da ya ke jawabi gabanin fara gasar Eguavoen ya ce tawagar tuni ta fara shirin yadda za ta tunkari zakarun gasar har sau 7 a kasar Masar.

“Kasar Masar tawaga ce mai karfin gaske wanda hakan ya basu damar lashe gasar har sau 7, sai dai munata shirye-shirye da kuma shirin tun karar kasar,” a cewar Eguavoen yayin ganawarsa da gidan talabijin na kasa NFF

Mai shekaru 56 ya kara da cewa kungiyar na kuma shirin lashe gasar ta AFCON da tawagar ta dade bata lashe ba.

Tawagar Super Eagles dai za ta fara buga wasan farko da kasar Masar a wasan farko a ranar 11 ga wata a filin wasa na Stade Roumdé Adjia

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!