Connect with us

Manyan Labarai

Wakilin Jaridar Thisday Ya tsallake rijiya da baya

Published

on

A jiya da daddare ne wasu bata gari su kai wa wakilin jaridar Thisday Ibrahim Garba Shu’aibu hari anan Kano.

Ibrahim Shuai’bu wanda shi ne shugaban masu aikewa da rahotanni ta kasa reshen jihar Kano, na kan hanyar sa ne zuwa wata cibiyar kiwon lafiya dake unguwar Rijiyar Zaki yayin da ya gamu da su, bayan da suka tsayar da shi suka kuma kwace masa wayoyin sa baki daya da kudade.

Bayanin hakan na kunshe a cikin sanarwar da sakataren kungiyar Mustapha Hodi ya fitar cewa Ibrahim Garba ya tsallake rijiya da baya ganin yadda bata garin suka yi yunkurin kasha

Continue Reading

Labarai

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kano ya ziyarci gidansu matashin da dan sanda ya harbe

Published

on

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP. Habu Ahmed Sani ya kai ziyarar ta’aziyya gidansu matashinnan marigayi Mus’ab Sammani da wani dan sanda ya harbe a makon da ya gabata, tawagar kwamishinan ta ziyarci gida dake unguwar Dantamashe a yankin karamar hukumar Ungogo dake nan Kano a safiyar yau.

CP. Habu Ahmed Sani ya bayyana cewa, yana kan hanyar sa ta zuwa birnin tarayya Abuja don hallatar wani muhimmin taro sai ya samu labarin faruwar al’amarin, kuma nan take ya juyo zuwa Kano inda ya bada umarnin fara bincike kan lamarin.

Ya zuwa yanzu tuni aka cafke dan sandan da ake zargi kuma an gurfanar da shi a gaban kotun ‘yan sanda domin girbar abinda ya shuka.

Kwamishinan ya kara da cewa, mutuwar matashin ba rashi bane ga iyayensa kadai har ma ga al’ummar Kano baki daya, adon haka za suyi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da daukar mataki akai.

Hoto a yayin ziyarar

Tun faruwar al’amarin dai mataimakan kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Kano sun kai ziyarar ta’aziyya gidan su marigayin.

Yayin ziyarar ta kwamishinan

Shima a nasa bangaren, mahaifin marigayin wato Mus’ab, Alhaji Sammani yayi godiya matuka tare da jinjinawa rundunar ‘yan sanda kan kokarin da take yi na bibiyar wannan al’amari, domin hukunta wanda ake zargi.

Sannan ya kara da cewa mutuwa karar kwana ce ga duk wanda ya kwanansa ya kare.

Labarai masu alaka:

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano

Published

on

Gwamnan Jihar Kano Abdullah Umar Ganduje ya sanar da nadin Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi II a matsayin shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano.

A wata sanarwa da sakataran yada labarai na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Abba Anwar ya fitar tace nadin Malam Muhammad Sunusi II zai fara aiki daga ranar litinin 9 ga watan Disambar da muke ciki.

Sanarwar tace sauran Sarakunan da Gwamnatin Kano ta kirkiro da suka hada da Sarkin Rano Tafida Abubakar ILa da Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II da Sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir da Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero Mambobi ne na sabuwar majalisar Sarakunan ta Jihar Kano.

Sanarwar da Abba Anwar ya fitar ta kara da cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci shugaban majalisar Sarakunan Jihar ta Kano kuma Sarkin Kano da ya kaddamar da sabuwar majalisar Sarakunan da Gwamnatin ta kikiro.

Shi dai shugabancin majalisar Sarakunan ta Jihar Kano zai rika zagayawa ne duk bayan shekaru biyu tsakanin Sarakunan na Jihar Kano.

Daga yanzu Malam Muhammad Sunusi II zai shugabanci majalisar Sarakunan daga nan zuwa shekarar 2021.

Continue Reading

Manyan Labarai

Wani matashi Mai shekaru 38 ya yanka rago da canza sunan sa zuwa Muhammad Buhari

Published

on

An gudanar da bikin sunan wani matashi mai shekaru talatin da takwas a Duniya a nan Kano daya sake sunan sa zuwa sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Matashin mai suna Muhammad Ibrahim dake Unguwar Gidan zoo yace ya canza sunan sa ne sakamakon kaunar da yake yiwa shugaban Kasa Buhari wanda hakan yasa ya siyo katon Rago ya yanka ya kuma rarraba Alewowi ga mutanan da suka halarci taron bikin sauya sunan nasa daya gudana a yau zuwa na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Matashin daya sauya sunan sa zuwa na shugaban kasa Buhari yace ko kadan ba siyasa ce tasa ya sauya sunan sa daga Muhammad Ibrahim zuwa Muhammad Buhari ba , ya sake sunan sane saboda zunzurutun kaunar da yake yi ga Buhari , bugu da kari kuma kowa yasan Shugaban kasa Buhari ba Barawon dukiyar al’ummar Najeriya bane.

Muhammad Ibrahim daya sake sunan sa zuwa Muhammadu Buhari yace zai canza sunan duk wasu muhimman takardunsa da suke dauke da tsohon sunan sa zuwa sabon sunan sa domin ya cigaba da amfani dasu , duk da cewa shi dan kasuwa ne dama.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa mutane da dama ne suka halarci bikin sake sunan Muhammad Ibrahim zuwa sabon sunan sa a yanzu wato Muhammad Buhari.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.