Connect with us

KannyWood

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Published

on

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Fitacciyar jarumar fina-finan hausa Maryam Yahya ta bayyana cewa rashin miji shi ne abinda ya hana ta yin aure.

Maryam Yahya ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tayi da Freedom Radio inda tace.

“da aure da mutuwa duk lokaci ne, idan lokaci na yayi ai zan daga, babu mijin ne, ku fito ku aureni, rashin miji ne ya hanani yin aure, kun san maza na wuya yanzu”

Hotuna dai sun yi ta yawo a shafukan sada zumunta inda aka rika cewa an kasa Maryam Yahya a wajen saurayinta fitaccen mai shirya fina-finan nan wato Abubakar Bashir Maishadda, a don haka tasha alwashin kin kara yin soyayya, sai kuma kwatsama aka ji wannan sabon batu ya fito daga bakinta.

Saurari cikakkiyar tattaunawar da Freedom Radio tayi da jarumar

Sai dai a wata tattaunawa da Freedom Radio tayi da Abubakar Bashir Maishadda ya tabbatar mana da cewa tabbas a baya sun yi soyayya da Maryam, amma Allah ne bai yi zai aure ta ba, domin a yanzu haka ma an kusa bikinsa kamar yadda ya shaida mana.

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Maryam Yahya da Abubakar Maishadda

Matashiyar Jarumar dai tana daga cikin manyan jarumai da tauraruwar su ke haskawa a masana’antar fina-finan Hausa a wannan loakci.

Idan baku manta ba dai, a kwanakin baya wani bidiyo da yayi ta yawo a shafukan sada zumunta na zamani ya nuna jarumar cikin kayan bacci, wanda bama ta san ana daukarta a hoton ba.

Masoyan Maryam sunyi Allah wadai da yada wancan bidiyon.

Haka ma dai a watannin da suka gabata jarumar ta je kasar Saudia inda suka hadu da fitaccen dan wasan kwallon kafar nan wato Pogba inda aka hasko Maryam tana ta ihu ta ga Pogba.

Wannan shima dai wani batu ne da ya mutsa hazo a tsakanin masu amfani da dandalin sada zumunta masu goyon baya da kuma masu sukan ta.

Rubutu masu alaka:

Kishiya da rashin kudi ne za su hana ni auren Yawale -Rayya

Na taba yin soyayya da Maryam Yahaya a baya –Mai Shadda

Nafi so na fito a matsayin fitsararriya a film -Maryam Yahaya

KannyWood

Muna yin Fina-finai ne dai-dai da addini Musulunci -Inji Furodusa

Published

on

Fitaccen mai shirya fina-finan Hausar nan Sani Ali Abubakar Indomie ya bayyana cewa fina-finan da sukeyi suna yinsu ne dai-dai da addinin Musulunci.

Sani Indomie ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan sabon film din da ya shirya na “Karamin Sani” inda yace kacokan wannan shiri ya mayar da hankali ne kan koyar da al’umma kaidata ubangiji madaukakin sarki wato Tauhidi.

“Acikin fina-finai na babu rawa kuma babu kida, saboda ya dace da tsari irin na addinin Musulunci” a cewar Abubakar Indomie.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da wasu al’umma ke kallon masu shirya fina-finan Hausar na wuce makadi da rawa wajen tsikarar al’ada da addinin malam bahaushe.

Continue Reading

KannyWood

Kun san jaruman da sukafi yawan mabiya a Kannywood?

Published

on

Dandalin sada zumunta na Instagram shi ne shafin da jarumai da kuma masu hurda da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sukafi maida hankali akan sa.

Babu shakka ga duk wanda ke neman wata gulma ko tsokaci game da masana’antar Kannywood to kawai yayi amfani da shafin Instagram domin ganin dukkan wainar da ake toyawa a masana’antar.

A yayinda shekara ta 2019 ke bankwana Freedom Radio ta bibiyi manyan jaruman dake amfani da dandalin na Instagram inda muka zakulo muku mutane goma sha daya da suke da yawan mabiya a masana’antar.

(more…)

Continue Reading

KannyWood

Hotunan fitsara: Rahma Sadau ta ce ita ba ‘yar Kano ba ce- Kannywood

Published

on

Shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai, ya ce matsalar da suke fuskanta game da daukar mataki kan jarumar nan ta masana’antar Kannywood Rahma Sadau cikin wani yanayi marar kyan gani abin kyama ita ce jarumar ta yi ikirarin cewa ita fa ba ‘yar Kano bace saboda haka ba su da iko akanta.

Sai dai ya ce kungiyar za ta ci gaba da sa ido kan jarumar domin gano gaskiyar ikirarin da ta yi.

“Matukar muka gano cewa tana karkashin ikon mu ba zamu bata lokaci ba wajen daukar matakin ladaftarwa akanta”

“Ba zamu saurara mata Ina tabbatar muku matukar ta yi kokarin shirya film a yankin da muke iko wato nan jihar Kano.

“Amma a yanzu bamu da iko saboda bazan iya yin hukunci a wata jiha ba saboda suma da nasu shugaban cin”

wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewar,sShugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewar  reshen jihar Kano, ya bayyana hakan ne a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a yau Lahadi goma sha biyar ga watan Disamba.

A baya-bayan nan ne dai wasu hotuna da faifan bidiyo da su ka yi ta yawo a kafafen sada zumunta na Facebook da Instagram, aka hango jarumar cikin wani yanayi shiga marar kyan gani na rashin da’a tana ta taka rawa, inda wani sassa na jikinta musamman ta kafarta duk a waje yake.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!