Connect with us

KannyWood

An fara sulhu tsakanin jaruman da suka yi auren mutu’a

Published

on

Fitacciya a kafar sadarwa ta Instagram Sadiya Haruna ta bayyana cewa ta dauki shawarar da wasu daga cikin jaruman masana’antar Kannywood suka bata, kan ta daina magana bisa dambarwar da ta kaure tsakaninta da jarumi Isa A. Isa.

Sadiya Haruna ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram, inda ta gode wa jaruma Hadiza Gabon tana mai cewa “Aunty Hadiza Gabon a koda yaushe ina alfahari da ke wallahi tallahi kalmominda kika gaya mun sun fi million 100 a gurina”.
Sai ka shiga matsala ne zaka gane mai sonka.
Kuma insha Allah ba zan sake cewa komai ba akan wannan batun nagode sosai ‘yar uwa”.

A jiya Lahadi ne jami’an ‘yan sanda a jihar Kano suka bada belin Sadiyar bayan da suka kamata bisa korafin da jarumi Isa A. Isa ya shigar kan zargin ta ci zarafinsa.

Rubutu masu alaka:

Kun san abinda ya biyo bayan komawar Aisha Buhari Villa?

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood

A zantawar Freedom Radio da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da bada belin nata yana mai cewa, rundunar za ta cigaba da bincike kan lamarin.

Sai dai a wani sautin muryar waya dake yawo a kafafen sada zumunta ya bayyana muryar Isa A. Isa din inda yake cewa kotu ce kawai zata raba su da Sadiyar bisa kazafin da tayi masa.

Haka ma dai wani bidiyon kira (video call) dake yawo a shafukan na sada zumunta sun nuna Sadiyar tana tattaunawa da wani, inda take musanta cewa ‘yansanda sun kama ta.

KannyWood

Muna yin Fina-finai ne dai-dai da addini Musulunci -Inji Furodusa

Published

on

Fitaccen mai shirya fina-finan Hausar nan Sani Ali Abubakar Indomie ya bayyana cewa fina-finan da sukeyi suna yinsu ne dai-dai da addinin Musulunci.

Sani Indomie ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan sabon film din da ya shirya na “Karamin Sani” inda yace kacokan wannan shiri ya mayar da hankali ne kan koyar da al’umma kaidata ubangiji madaukakin sarki wato Tauhidi.

“Acikin fina-finai na babu rawa kuma babu kida, saboda ya dace da tsari irin na addinin Musulunci” a cewar Abubakar Indomie.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da wasu al’umma ke kallon masu shirya fina-finan Hausar na wuce makadi da rawa wajen tsikarar al’ada da addinin malam bahaushe.

Continue Reading

KannyWood

Kun san jaruman da sukafi yawan mabiya a Kannywood?

Published

on

Dandalin sada zumunta na Instagram shi ne shafin da jarumai da kuma masu hurda da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sukafi maida hankali akan sa.

Babu shakka ga duk wanda ke neman wata gulma ko tsokaci game da masana’antar Kannywood to kawai yayi amfani da shafin Instagram domin ganin dukkan wainar da ake toyawa a masana’antar.

A yayinda shekara ta 2019 ke bankwana Freedom Radio ta bibiyi manyan jaruman dake amfani da dandalin na Instagram inda muka zakulo muku mutane goma sha daya da suke da yawan mabiya a masana’antar.

(more…)

Continue Reading

KannyWood

Hotunan fitsara: Rahma Sadau ta ce ita ba ‘yar Kano ba ce- Kannywood

Published

on

Shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai, ya ce matsalar da suke fuskanta game da daukar mataki kan jarumar nan ta masana’antar Kannywood Rahma Sadau cikin wani yanayi marar kyan gani abin kyama ita ce jarumar ta yi ikirarin cewa ita fa ba ‘yar Kano bace saboda haka ba su da iko akanta.

Sai dai ya ce kungiyar za ta ci gaba da sa ido kan jarumar domin gano gaskiyar ikirarin da ta yi.

“Matukar muka gano cewa tana karkashin ikon mu ba zamu bata lokaci ba wajen daukar matakin ladaftarwa akanta”

“Ba zamu saurara mata Ina tabbatar muku matukar ta yi kokarin shirya film a yankin da muke iko wato nan jihar Kano.

“Amma a yanzu bamu da iko saboda bazan iya yin hukunci a wata jiha ba saboda suma da nasu shugaban cin”

wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewar,sShugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewar  reshen jihar Kano, ya bayyana hakan ne a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a yau Lahadi goma sha biyar ga watan Disamba.

A baya-bayan nan ne dai wasu hotuna da faifan bidiyo da su ka yi ta yawo a kafafen sada zumunta na Facebook da Instagram, aka hango jarumar cikin wani yanayi shiga marar kyan gani na rashin da’a tana ta taka rawa, inda wani sassa na jikinta musamman ta kafarta duk a waje yake.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!