Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood

Published

on

Wata sabuwar dambarwa ta barke a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood tsakanin jarumi kuma mashiryin fina-finan Hausa wato Isa I. Isa da kuma jaruma Sadiya Haruna wadda tayi kaurin suna a shafukan soshiyal midiya.
Dambarwar dai ta faro asali ne biyo bayan zarge-zargen da Sadiyar ta jefa kan jarumin, tun kafin ta kama sunansa, wanda a karshe kuma ta kama sunansa.
Daga cikin zarge-zargen dai akwai cewa sunyi auren mutu’a (auren sha’awa) a cewar ta cikin wani bidiyo da ta saki.
Jarumar ta kalubalanci jarumin da ya fito ya kare kansa game da kalubalantarsa da tayi.

Rubutu masu alaka:

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Wakilin Jaridar Thisday Ya tsallake rijiya da baya

Sai dai shima jarumin tuni ya wallafa wani bidiyo a shafinsa inda yake bayyanawa duniya cewa ya aikata wasu abu na ba dai-dai ba da yake neman gafarar al’umma, daga bisani ya goge bidiyon daga shafinsa, amma ina tuni bidiyon ya karade dandalin YouTube.
A kwanakin baya dai jarumin yayi wani bidiyo da yake bayanin cewa ana ta tambayarsa shin meye alakarsa da Sadiya Haruna?, inda ya bayyanawa duniya cewa matarsa ce.
Sa’o’I uku da suka wuce Sadiyan ta wallafa a shafinta na Instagram cewa Isa ya kawo mata ‘yansanda har gida kamar yadda kuke gani a kasa.


A kwanakin baya ma dai an tafka makamanciyar irin wannan dambarwa a tsakanin Sadiyan da kuma wasu jaruman fina-finan, inda ta zargi wasu daga ciki da aikata badala.
Sai dai jaruma Teema Makamashi ta kalubalance ta inda ta bayyana cewa jami’an tsaro sun samu nasarar cafke Sadiyan a ofishin jarumin Isa A. Isah.
Ita ma dai daya daga cikin manyan jaruman dake taka leda a soshiyal midiya Muneerat Abdussalam ta bayyana mamakinta da faruwar wannan rikici, inda ta bayyana Sadiya da Isa matsayin wasu masoyan biyu da suka taba kai mata ziyara.
Allah ya kyauta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!