Labarai
Dan Hisba ya ki karbar rashawa
Wani Jami’in hukumar Hisba mai suna Nuhu Muhammad Dala, ya ki amincewa da karbar cin hancin naira 100,000 daga hannun wani matashi mai sana’ar sayar kayan maye da nufin rufa masa asiri.
jami’in Hisban, wanda shi ne mataimakin kwamandan hukumar na karamar hukumar Dala, ya ki karbar cin hancin ne daga ‘yan uwan matashin wanda kwararre ne wajen sayar da kayan maye inda kuma ya kama shi da su dumu-dumu.
‘yan uwan matashin dai sun bukaci da a boye labarin kama kayan mayen ne inda suka bashi tsabar kudin, shi kuma da karbarsa sai ya sanar da hukumar.
A zantawar Freedom Radio da mataimakin kwamandan hukumar ta Hisba na jihar Kano mai kula da ayyuka na musamman Malam Shehu Tasi’u Ishaq, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa za’a hada mai laifin da kuma kudin da suka bayar a kuma gurfanar da su a kotu.
Malam Shehu Tasi’u Ishaq, ya kuma yaba wa jami’in nasu bisa namijin kokarin nasa na kin sakin kayan mayen.