Connect with us

Labarai

Hisbah ta cafke matashin da yayi kalaman batanci

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gurfanar da wani matashi mai suna Umar Farouq mazaunin unguwar Sharada bisa zargin yin batanci ga Allah (s.w.a).

Hukumar Hiisbah ta gurfanar da matashin a babbar kotun shari’ar musulunci dake Hausawar gidan Zoo a nan Kano.
A yayin zaman kotun na yau Laraba an karantawa wanda ake zargin lafin sa kuma nan take ya amsa.

Wakilin mu Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito mana cewa mai shari’a Ali Kani ya dage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Afrilu mai zuwa sannan ya aike da wanda ake zargi zuwa gidan gyaran hali.

Shi ma a nasa bangaren mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah Malam Tasi’u Ishaq ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa al’ummar unguwar Sharada ne suka yi wa Hisbah ko rafi kan yadda matashin ke cin zarafin mahalicci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!