Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar NATCA ta koka

Published

on

Kungiyar masu kula da zirga-zirga jiragen sama ta Najeriya, wato Nigerian Air Traffic Association, ta koka gameda rashin isasun kayayyakin aiki tsakanin su da matuka jirage, wanda hakan ke kawo tarnaki ga ayyukan su.

Mataimakin shugaban kungiyar Ahmed Adamu ne, ya bayyana hakan jim kadan bayana kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, wanda ya maida hankali kan yadda kungiyar ke gudanar da ayyukanta.

Ya kara da cewa, kungiyar na kula da jiragen sama tun daga tashi zuwa sauka, domin tabbatar da an samu nasarar tashi da sauka cikin kwanciyar hankali.

A nasa bangaren, daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar, Malam Husaini Jibril  ya ce, kungiyar na fuskantar kalubale ta hanyar rashin isassun ma’aikata sakamakon wahalar da dalibai da ke karantar aikin nasu ke fama da shi.

Bakin sun yi kira ga gwamnati kan ta taimaka wajen kawo musu isassun kayayyakin aiki, da daukar nauyin dalibai masu karatun ilimin tukin jiragen  sama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!