Connect with us

Labaran Kano

Garin da ake aure akan naira dubu hamsin (N50,000) kacal a Kano

Published

on

Garin da ake aure akan naira dubu hamsin (N50,000) kacal a Kano

Dagacin garin Kera dake karamar hukumar Garko a nan Kano ya sanya dokar kayyade kudin aure da sadaki baki daya akan kudi N137,000 ga budurwa, bazawara kuma N50,000.

Kusan watannin uku kenan da dagacin Mallam Bello Musa ya sanya wannan doka, sai dai wasu daga al’ummar garin sun koka bisa wannan sabon tsari.

A zantawar da Freedom Radio ta yi da wasu iyaye a garin sun bayyana cewa ko kadan ba za su lamunci wannan tsari ba a don haka sun shirya tsaf domin kai kokensu gaban hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano.

Haka kuma Freedom Radio ta tuntubi dagacin wanda ya bayyana cewa wannan doka fa sun yanketa ne domin samar da masalaha a garin, kuma al’umma da malaman garin duka sun amince da wannan doka.

Idan zaku iya tunawa dai a watan Janairu na shekara ta 2017 mahukunta a karamar hukumar Danbatta dake nan Kano, suma suka kaddamar da dokar kayyade aure sai dai ta samu cikas a karshe.

Rubutu masu nasaba:

Amarya ta haihu bayan wata hudu da Aure

An gurfanar da uba da ‘yarsa gaban kotu bisa zargin shirya auren bogi

Continue Reading

Labarai

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kano ya ziyarci gidansu matashin da dan sanda ya harbe

Published

on

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP. Habu Ahmed Sani ya kai ziyarar ta’aziyya gidansu matashinnan marigayi Mus’ab Sammani da wani dan sanda ya harbe a makon da ya gabata, tawagar kwamishinan ta ziyarci gida dake unguwar Dantamashe a yankin karamar hukumar Ungogo dake nan Kano a safiyar yau.

CP. Habu Ahmed Sani ya bayyana cewa, yana kan hanyar sa ta zuwa birnin tarayya Abuja don hallatar wani muhimmin taro sai ya samu labarin faruwar al’amarin, kuma nan take ya juyo zuwa Kano inda ya bada umarnin fara bincike kan lamarin.

Ya zuwa yanzu tuni aka cafke dan sandan da ake zargi kuma an gurfanar da shi a gaban kotun ‘yan sanda domin girbar abinda ya shuka.

Kwamishinan ya kara da cewa, mutuwar matashin ba rashi bane ga iyayensa kadai har ma ga al’ummar Kano baki daya, adon haka za suyi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da daukar mataki akai.

Hoto a yayin ziyarar

Tun faruwar al’amarin dai mataimakan kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Kano sun kai ziyarar ta’aziyya gidan su marigayin.

Yayin ziyarar ta kwamishinan

Shima a nasa bangaren, mahaifin marigayin wato Mus’ab, Alhaji Sammani yayi godiya matuka tare da jinjinawa rundunar ‘yan sanda kan kokarin da take yi na bibiyar wannan al’amari, domin hukunta wanda ake zargi.

Sannan ya kara da cewa mutuwa karar kwana ce ga duk wanda ya kwanansa ya kare.

Labarai masu alaka:

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Continue Reading

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta sake salo wajen kubutar da yaran Kano

Published

on

Dr Bashir Adamu Aliyu

Gamayyar Kungiyoyin  rajin kare hakkin al’umma a jihar Kano sunyi kira da babbar Murya ga gwamnatin Kano data kara kaimi wajen ganin ta kubutarda sauran yaran da aka sace domin dawo dasu cikin iyalansu.

Sakataren Gamayyar Kungiyoyin na Jihar Kano Injiniya Bashir Adamu Aliyu ne ya bayyana hakan lokacin taron da kungiyoyin suka shirya domin duba lafiyar iyayen yaran da basu magun guna kyauta tare da basu shawarwari ta fuskar shari’ah.

Bashir Adamu Aliyu ya kuma kara da cewa abun takaicine a cigaba da zuba idanu ana cigaba da satar kananan yara a Kano tare da canza musu addini , a don haka ya zama wajibi gwamnati ta kara matsa kora domin gano ko su waye.

Da take nata Jawabin a yayin taron Barista Sadiya Adamu Aliyu cewa tayi adadin yaran da aka sace ya karu don kuwa izuwa yanzu sama da iyayen yara dari ne suka shigar musu da korafin cewa an sace musu yaran su.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito iyayen yara da dama ne suka halarci taron daga unguwanni daban daban wadanda aka sacewa yara sun kumayi fatan gwamnati ta yi gaggawar gudanarda buncike domin gano sauran yaran su da aka sace sakamakon mawuyacin halin damuwar da suke ciki.

Continue Reading

Labarai

Sarkin askar Kano ya kalubalanci likitoci akan yi wa maza shayi

Published

on

Sarkin Askar jihar Kano Ahaji  Dakta na Bango ya kalubalanci likitoci akan su daina sukar salon yi wa maza shayi da suke yi su.

Alhaji Dakta na bango ya bayyana hakan ne a yayin da ya kira taron manema Labarai domin nuna takaicinsa  kan  irin kallon raini da Likitoci suke yiwa sana`arsu.

A cewar sa sun gada ne tun iyaye da kakanni  ba wai da rana tsaka kawai suka shiga sana`ar ba.

Sarkin Kano ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya su yi aiki kafada-da-kafada da hukumar ilimin manya

Ka zalika sarkin Askar ya bayyana bambamcin sana`ar tasu da ta likitoci yana mai buga misali da bambancin Kazar gida da Kazar gidan gona.

Na Bango ya  kara da cewa a kasashen da aka cigaba likitan turawa  basa sukar masu magugunan gargajiya,ko kuma su kan su  masu maganin gargajiya su soki magugunan turawa.

Yana mai cewar akan haka ya zama wajibi likotoci su dena sukar kai tsaye su don kuwa su basa yi.

Sarkin Askar ya kara da fadar bambanci akan shayi,inda yace shayi ya kasu a kalla kala Goma, kuma  bambanci sosai a tsakanin Shayin asibiti da na gargajiya.

 

 

 

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.