Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin Tazarcen Buhari: Mai yasa Osinbajo yake shan mazga?

Published

on

Tun lokacin da shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahamud Yakubu ya ayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2019, sannan aka rantsar da shugaba Buhari a karo na biyu a ranar  29 ga watan Mayu na shekarar bana.

Bayan rantsar da shugaba  Buharin a ranar 29 ga watan Mayu yake shaidawa manema labarai cewa da ya kammala wa’adin sa na biyu a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023 zai tattara ya nasa ya nasa ya koma birnin Daura wadda itace mahaifar shugaban kasar.

Wannan Magana ta shuagab Buhari ba kowa ne yayi mata wata fasssara ba, saboda an san abu ne sananne da ya kamata ace duk shugaban da ya  ke kammala wa’adi na biyu kaida ne ya tattara kayansa ya bar fadar  Gwamnatin ta tarayya.

Shi dai tsarin mulkin Najeriya ya bawa shugaban kasa da Gwamnoni wa’adin mulki na tsawon shekara hudu, idan an sake zaben sa yayi mai mai wanda hakan yana nufin shekara takwas kenan.

Yunkurin zarce wa’adin mulki da shugabannin Najeriya ke yi, ba wai wani abu ne sabo ba, daga ciki shugabannin mulkin soja ma sun so su dare a mulkin kasar nan amma hakan bai yi nasara ba.

Tun dai rantsar da shugaba Buhari kimanin watanni shida da suka gabata ake zargin cewa shugaba Buhari na kokarin wuce wa’adin mulkin da tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya deba masa wato shekaru takwas kacal.

Wannan rade rade dake faruwa na tazarce ,haka aka zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda shi ma yukurin na sa bai nasara ba.

 

Amma wani abu mai kama da juna ,sanda aka zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da neman mulkin  Najeriya a karo na uku ya rika mazgar mataimakin sa Atiku Abubakar ta hanyar dakile shi a bangarori na siyasa da mukamai da harkokin siyasa har sai da ta kai ya cire masa dogari.

A yanzu ma, daga rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari sai ga shi hakan ta fara faruwa ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

A wa’adin shugaban kasa Muhammadu  Buhari na farko da ya fara daga watan Mayun shekarar 2015 zuwa shekarar 2019 inda ya kammala a shekarar bana ,shugaba Buhari ya bawa mataimakin sa damammaki inda shirin nan na samarwa matasa aikin yi yake karkashin Ofishin mataimakin sa Osinbajo, amma bayan sake rantsar da su, sai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da shirin samarwa matasa aikin yi na N-Power zuwa ga sabuwar maaikatar jin kan al’umma.

A wa’adin farko  kwamitin tattalin arzikin Najeriya yana karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi  Osinbajo sai kuma kwatsam kwannan a wa’adin su na biyu  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake kafa wani kwamiti  wanda zai rika ba shi shawara akan harkokin tattalin arziki wato Economic Advisory council.

Shugaba Buhari ya  dorawa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Farfesa Charles Chukwuma Soludo a matsyin sabon shugaban kwamitin tattalin arzki na gwamnatin ta sa sabuwa.

Kuma abun mamakin shi ne wannan sabon kwamiti da Farfesa Charles Soludo zai shugabanta zai rika kai rahotan sa ne kai tsaye ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan mazga da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke sha daga ofishin mai gidansa shugaba Muhammadu Buhari ta bar baya da kura .

Inda ko a kwanakin nan ma sanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi hutu birnin Landan daga ranar 1 ga watan Nuwamban da muke ciki shugaban kasar ya tube mai taimakawa mataimakin sa Yemi Osinbajo su kimanin 35 .

Ta kai hatta sa hannu na wasu dokoki sai da aka bi  shugaba Buhari har zuwa birnin Landan ya saka hannu wanda a da ba haka bane.

A wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari na farko ya kan mika wasika cewa mataimakin sa ne mukaddashin shugaban kasa ,amma a wannan karo da yayi hutun kwana kusan goma sha shida a kasar Burtaniya Farfesa Yemi Osinbajo a mataimakin shugaban kasa ya tabbata.

Amma a wa’adin farko sai shugaba Buhari yak an bawa mataimakinsa damar zama mai rikon mukamin shugaban kasa ko na kwanaki biyar inda ya bar doron Najeriya ya tafi ziyarar kashin kai musamman ma Burtaniya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!