Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar KAROTA ta nemi a kebe mata Naira biliyan guda

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgan ababan hawa ta jihar Kano KAROTA ta sake sanya Naira dari 100 a matsayin kudin haraji ga duk wani mai baburin Adai-adaita sahu.

Babban manajan daraktan hukumar Baffa Babba Dan Agundi ya bayyyana hakan jim kadan bayan kare kunshin daftarin kasafin kudin badi a gaban kwamitin kula da gidaje da sufuri na majalisar dokoki ta jiha.

Baffa Babba Dan Agundi ya ce hukumar ta KAROTA na sanya ran cewa zata samar da kudaden shiga na Naira biliyan shida ta hanyar yin rijista ga masu baburan Adai-adaita sahu da kuma sauran wasu motocin hanya.

Haka zalika shugaban na KAROTA ya ce tuni masu baburan Adai-adaita sahun suka fara biyan Naira dari kullum ga gwamnatin jiha, yana mai cewa ba wai hukumar kawai zata dinga karbar kudaden haraji a hannun masu motocin hanya ba, a’a har ma da sauya tunani masu take dokokin toki, da wayar da kan su.

Iftila’i: Dan KAROTA ya rasa ran sa

‘Yan sanda sun cafke sojoji kan KAROTA

An dambata tsakanin KAROTA da Sojoji

Baffa Dan-Agundi ya kuma kara da cewar nan bada jimawa ba hukumar ta KAROTA zata kaddamar da sanya na’urar takaita gudu a baburan masu kafa uku.

Ya ce hukumar zata aiwatar da wannan tsarin ne don kama bata gari da kuma rage ayyukan fashi da makami ne, biyo bayan shawarar da gwamnati ta yanki kan yadda ake yawan kuka da masu baburan Adai-adaita sahu.

Babban manajan darakatan hukumar ya kara da cewar hukumar ta nemi da a kebe mata Naira biliyan guda cikin kasafin kudin shekara ta 2020.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!