Connect with us

Labarai

SACA: kimanin kaso 35 cikin dari masu dauke da cutar HIV ke karbar magani

Published

on

Cuta mai karya garkuwa

Babban daraktar a hukumar da ke kula da masu dauke da cuta mai karya garkuwa wato AIDS Sabitu Shanono ya ce kaso 35 cikin dari na masu dauke da lalurar HIV/AIDS dake jihar Kano na amfani da magunguna a fadin jihar.

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewar shugaban hukumar kuma likita Dr Shanono , ne ya bayyana haka a yayin da yakai ziyara fadar mai martaba sarkin Karaye  Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu a fadarsa.

Dr Shanono da yake kaddamar da watan wayar da kan masu dauke da lalurar ya ce hukumar da ke lura da masu dauke da cuta mai karya garkuwa HIV/AIDS zata fara wannan gangami ne a masarautar Karaye a mako mai kamawa.

Daraktan ya ce gangamin wayar da kan zai bada gwajin da akeyiwa masu juna biyu a asibitocin mata masu juna biyu.

Ya kuma bukaci goyon bayan masarautar Karaye wajen yaki da cuta mai karya garkuwa jiki.

Da yake agana sarkin Karaye Alh Ibrahim Abubakar ya jadadda goyon bayan masarauta domin tabbatar da an rage yaduwar cuta mai karya garkuwa.

Ya kuma bukaci alumma da su tabbata sun hallarci taron domin tantance kansu basa dauke da cuta mai karya garkuwa.

 

 

 

Inda Ranka

Kotu ta saida gidan wani mutum yana gidan gyaran hali

Published

on

Duk da cewar bayan ya fito ya kai shigar da kara har ma kotu ta bada  umarni amma hakonsa bai cimma ruwa ba, domin masu gwanjan babbar kotun jiha sun bujirewa umarnin ta

Wakilin mu Nasiru Salisu Zango ya rawaito cewa, a cikin kunshin bayanan shari’a wanda alkali Faruq na kotun kasuwa ya rubuta ya nuna cewa, irin hukunce-hukuncen da kotun ta bada umarni amma wadanda ake kara suka yi mirsisi  a don haka kotun ta bayyana cewar matakin ya zama rainin-wayo.

Kamar yadda labarin ya nuna cewa wani mutumi ne wanda karayar arziki ta same shi har ta kai ga cin bashin da aka kai shi kurkuku saboda ya gaza

Wanda yana cikin wannan  kadamin ne sai aka sake kai karar sa kotun kasuwar Kurmi  saboda wadansu kudadan da ake binsa,duk da cewar an je wannan kotun kasuwar don tabbatar da sulhun da aka cimma a tsakanin su kama yadda hukuncin kotun ke tafiya akai,  amma sai shari’ar ta sauya zane daga batun sulhu ta dawo karbar kudi.

Kai-tsaye : Yaushe ne za’a cigaba da sauraran shari’ar Ganduje da Abba?

Kotun daukaka kara ta sanya ranar shari’ar Ganduje da Abba

Kotu a Kano ta yankewa mai cin zarafin kananan yara hukunci

Haka shima wanda ake bi bashin Malam Bashir Fari Sharada ya bayyana cewa ,daga wannan ranar da kotun ta sulhuntasu bata kara neman sa ba, amma hakan alkali yayi hukuncin zuwa asayar da gidan sa ba tare da sanin sa ba.

Ya sake bayyana cewa, yana zauna ne da iyalin sa suna karin kumallo kwatsam sai sukaji an sako kai cikin gidan ana fatali da kayansu.

Akan haka ne Malam Bashir Fari Sharada ya  bayyana bakin cikinsa duba da cewa wadanda aka je da su gidan shi har da Kurame domin ba za su iya jin irin roko da magiyar da yake musu ba,

Ya kara da cewar irin tozarcin da su kai masa har ma takai da iyalisa su kwana a makwabta shi kuma ya kwana a shagon damin acewar sa maganar siyar da gidan sa ta tabbata.

Hakan yasa ya daukaka kara shida lauyansa domin dakatar da Alkalin Sharif daukar matakin yanke hukuncin a baya, amma hakan bai samu ba saboda an dauke  alkalin kotun wanda ya yanke hukuncin farko.

Amma  kakakin babbar kotun jihar Kano Baba jibo Ibrahim ya ce alkalin babbar kotun jiha ya mayar da martanin cewa har idan wannan korafi yaje waje sa sai abin da ya tubewa buzu nadi.

Continue Reading

Labarai

Wani dan kasuwa ya gamu da ajalinsa sakamakon harbin bindiga

Published

on

Dan sandan  dai yana gadi ne a wani Banki  yayin da ya hango wannan mai mota ya buge wani mutum kuma wasu ‘yan sanda dake aiki a bakin titi suka  bukaci shi daya bude motarsa a saka wanda yaji raunin amma kuma yaki bayan da aka yi zargin cewar yana son ya tsere.

Amma sai yaki bin umarnin su hakan ya sanya dan sanda  dake zaune yana aikin gadi ya ja kunamar bindigarsa ya harbi wannan matukin motar kuma nan take ya rasu.

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Kano: Lauyoyi sun yi barazanar gurfanar da kwamishinan ‘yan sanda

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Hakan tasa abokin tafiyar direban ya kasa magana saboda dimaucewa da yayi ganin abinda yafaru da wanda suke tare.

Tuni dai tawagar ‘yan sanda suka halacci gurin da abin yafaru  karkashin jagorancin babban mukaddashin kwamishinan’ yan sanda na Kano mai lura da ayyukan yau da kullum DSP Balarabe sule.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP Abdullahi Haruna ya ce rundunar na tattara bayanai kafin gurfanar da wanda ake zargi a kotu

 

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Hukumar Hisbah ta ziyarci makarantar ‘yan mari ta zamani

Published

on

Babban kwamandan hukumar ta jihar Kano Sheik Harun Muhad Sani Ibn Sina da kuma baban daraktan hukumar Dr, Aliyu Musa Kibiya sun kai ziyarar aiki makarantar ‘yan Mari ta zamani dake karamar hukumar Kura anan jihar Kano wanda Asusun tallafawa na Annur ya kafa.

Makarantar ‘yan Marin ta zamani wanda Dr, Aliyu Musa Kibiya ya asasa da nufin karfafa samar da ingantaccen ilimi mussaman ma na Al-qur’ani mai girma don taimakawa a kokarin da gwamnati ke yi na ganin ana bada ilimin Al-qur’ani ta hanyar data dace a jihar Kano.

Haka zalika Tsangayar ko makarantar ‘Yan marin irin ta ce ta farko a jihar Kano da aka taba kafawa ta zamani.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’in yada labarai na hukumar ta Hisbah Lawal Ibrahim Fagge \ya sanya hannu cewa, tsangayar na da ajujuwa guda 27 da dakunan kwana na dalibai 35 da masallaci.

Hisbah na shirin kara inganta ayyukanta a kananan hukumomi

Laifin iyaye ne ke haifar da mace-macen aure -Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben barasa 196,400

Ana dai kyautata zaton cewar a kwanan ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje zai kaddamar da Tsangayar ta zamani a cikin wannan shekarar yayin da kuma  za’a koma karatu gadan-gadan nan bada jimawa ba.

 

 

 

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.