Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta bada umarnin rufe duk asibitin da ba shi da Rijista

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe dukkan asibitocin kuɗi da ba su da Rijista.

 

Kwamishinan lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bada wannan umarni yayin da ya ke buɗe taron bita da bada horo ga shugabanni da mamallaka asibitoci masu zaman kansu da ke nan Kano wanda hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu PHIMA ta shirya, ake gudanar da shi yanzu haka a yau Alhamis.

 

Ya ce, ɗaukar wannan mataki ya zama dole sakamakon yadda ake samun matsaloli wajen yadda asibitocin ba sa gabatar wa gwamnatin bayanan ayyukansu kama daga alƙaluma da bayanan mutanen da suka duba da sauransu.

 

Kwamishinan, ya ƙara da cewa, “A yanzu haka mutane da dama sun zaɓi riƙa tafiya asibitoci masu zaman kansu maimakon na gwamnati domin neman lafiya, sai dai da da dama daga cikin irin waɗannan asibitoci ba su da Rijista.

 

Don haka daga yanzunan, ina mai sanar da bayar da umarnin kulle duk wani asibiti da ke gudanar da aiki ba tare da cikakkiyar rijistar gwamnati ba.”

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!