Connect with us

KannyWood

Ni da Ali Nuhu laifunmu ne ke haifar da matsala a Kannywood –Adam Zango

Published

on

Featured Video Play Icon

Fitaccen jarumin fina-finan hausar nan Adamu Abdullahi wanda akafi sani da Adam Zango ya bayyana cewa yaran sa da yaran jarumi Ali Nuhu sune ke rura wutar rikici a masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood.

Cikin wata tattaunawa da jarumin yayi da gidan Radio France International (RFI) ya bayyana cewa rikici da matsalolin da yaran sa dana fitaccen jarumi Ali Nuhu ke haifarwa a Kannywood ba laifin kowa ba ne sai shi da jarumi Ali Nuhu.

A cewar Adamu Zango da ace suna tsawatarwa ga yaran nasu to da zasu iya dakatar da su daga yin duk wani abu da zai haifar da rikici a masana’antar.

Jarumi Adam Zango ya kara da cewa ta bangarensa bai yadda yaransa su ci zarafin wani jarumi ba.

Idan zaku iya tunawa dai a watannin baya ne wani rikici ya kunno kai tsakanin manyan jaruman guda biyu wanda har sai da ta kai ga anje kotu, inda daga bisani kuma aka samu yin sulhu a tsakanin su.

Labarai masu alaka:

Da gaske Adam Zango ya dauki nauyin karatun dalibai?

Jaruman Kannywood sun fara bayyana da Iphone 11

Ina fatan Allah ya bani sana’ar da tafi Kannywood -Mansur Makeup

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,467 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!