Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Rundunar Hisbah ta sabunta dokar han cakuda mata da maza

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bukaci gamayyar kungiyoyin direbobin Mashin mai kafa uku(A daidaita Sahu)da su guji ci gaba da cakuda Maza da Mata wajen gudanar da haya a Ababen hawansu daga 1 ga watan Janairun sabuwar Shekarar 2020 mai kamawa.

Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano Shaikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina shi ya bukaci hakan a lokacin da yake ganawa da gamayyar Kungiyoyin direbobin Babur mai kafa 3 da hukumar ta gayyato su domin sanar da su cewa an sabunta dokar nan da ta yi hani da cakuda Maza da Mata a cikin Ababen hawa.

Haka Kuma doka zata fara aiki daga ranar 1 ga watan sabuwar Shekara Mai kamawa, wato 20220

Shaikh Ibn Sina ya bayyana cewa an samar da wannan doka ne tun cikin shekara ta 2002,kawai dai an sake sabunta ta ne don ganin an tabbatar da babban aikin hukumar Hisbah na Umarni da kyakkyawa da kuma hani ga mummuna

Kasancewar yadda aka yi watsi da bin wannan doka,wanda kuma hakan ba karamar fitina yake haifarwa a cikin al’umma ba.

Hukumar Hisbah ta ziyarci makarantar ‘yan mari ta zamani

Mata sun kokawa hukumar Hisbah kan cin zarafin mazaje

Laifin iyaye ne ke haifar da mace-macen aure -Hisbah

Kwamandan na Hisbah ya ce daga wannan rana da aka ambata, dakarun Hukumar za su fito domin su tabbatar da cewa an bi wannan doka sau da kafa.Inda a matakin farko za a fara da yin nasiha, sannan kuma sai biyan tarar kudin da ba su gaza #5,000 ba ga duk wanda aka samu da laifin bijirewa wannan doka.

A nashi jawabin Shugaban gamayyar kungiyoyin direbobin  Babur mai kafa uku na jihar Kano,ya bayyana cewar za su sanar da dukkan Mambobinsu game da wannan doka,kuma a matsayin su na Musulmi suna goyon bayanta kuma za su bada dukkan hadin kan da ake bukata..

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!