Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane biyu

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba takwas karkashin jagorancin mai shari’a Usman na Abba  ta zartar da hukuncin kisa akan mutane biyu wanda ta samu da laifin kisan kai.

Tun a shekarar dubu biyu da sha uku ne  Gwamnatin jiha ta gurfanar dasu bisa zarginsu da laifin hadin baki , sata da kuma kisan kai, sai dai sun musanta zargin.

Lauyoyin gwamnati sun gabatar da shedu har guda shida, sai dai kotun bata yarda da shaidar wanda ake zargi na hudu ba inda ta sallame shi.

A cewar kotun  Aliyu Abubakar da Sanin Fulani  ta kamasu da laifin  dumu-dumu don haka tabada umarnin  a yanke musu hukuncin rataye.

Wasu gwamnatoci na yin burus da umarnin kotu- Barista Ibrahim Sule

Yau Ganduje da Abba kowa zai san matasayin sa-Kotun daukaka kara

Dole masu ruwa da tsaki su amince da hukuncin kotuna -Sarkin Kano

An kuma karawa Sanin Fulani daurin Shekaru Bakwai a gidan maza sak makon samun sa da kayan sata .

Haka kuma kotun ta ce bazata fadi ra’ayinta akan wanda ake zargi na farko ba wato Tasi’u  Abudullahi kasancewar ya rasu a gidan gyaran hali.

Amma daga baya kotu tawanke Kabiru Gayawa yayin da yayi tafiyar sa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!