Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Abinda sa ya Ganduje ya zabi Sarki Sunusi II jagoran sarakuna

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi na biyu matsayin shugaban majalisar sarakuna ta jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kano Abba Anwar ya fitar a yau litinin ta bayyana sarkin Kano matsayin shugaban majalisar sarakunan.

Dama dai a kunshin dokar da gwamnan ya sanya wa hannu na nuni da cewar shugaban majalisar sarakunan shi ne zai jagoranci majalisar masarautar na shekaru biyu wato za’a dinga yin tsarin karba-karba ne.

A cewar Abba Anwar nada Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Kano yayi dai-dai da doka ta 4 (2) (g) da sashe 5 (1) (2) na dokar masarautar Kano ta shekarar 2019.

Kazalika sanarwar ta ce daga cikin sauran ‘yan majalisar akwai dukkanin sarakunan jihar masu daraja ta daya, da suka hada da Bichi wanda Alhaji Aminu Ado Bayero ke jagoranta sai Rano wadda Abubakar Autan Bawo ke jagoranta da Karaye inda Alhaji Ibrahim Abubakar na II da kuma na Gaya Ibrahim Abdulkadir.

Idan zaku iya tunawa dai a makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan sabuwar dokar kirkirar sabbin masarautun a jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano

Sarkin Kano ya bude masallacin juma’a na sabuwar jami’ar Bayero

Ganduje ya musanta rahoton jihar Kano ce kan gaba a gurbacewar mahalli

Freedom Radio ta tuntubi Farfesa Kamilu Sani Fagge wani mai fashin baki akan al’amuran yau da kullum kuma masanin kimiyyar siyasar a jami’ar Bayero dake nan Kano inda ya bayyana cewa siyasace gwamnan yayi  amfani da ita wajen yin dabara don mutane su karbi kirkiro da masarautun.

Har ila yau farfesan ya kara da cewar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi hakan ne don kashe wasu rade-radin da ake yi ko zai nada sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban majalisar sarakunan,

Farfesa Fagge ya kara da cewa ta wani fuskar kuma so yake ya kashe zafin wutar don kada mutane suyi ta cece-ku-ce-ce kan batun.

Idan za’a iya tunawa dai wani ofishin lauyoyi a nan Kano ya bukaci gwanan Kano da majalisar dokoki da su jingine batun sake gyaran dokar kafa rusassun masarautun na Bichi, Karaye, Gaya, da Rano, wanda mai shari’a Usman Na’abba na babbar kotun jiha ya rushe makonni biyu da suka gabata .

Ofishin lauyoyin da suke wakiltar madakin Kano da mutum uku a kunshin sharia mai lamba K/ 197/2019 wadda take gaban babbar kotun jiha mai lamba uku karkashin mai shari’a Ahmad Tijjani.

 

Har ila yau, Cikin wadanda ake kara a wannan sharia sun hadar da shugaban majalisa da baturen sharia da gwamnatin Kano.

Haka kuma, a ranar Alhamis ne majalisar dokoki ta jihar Kano ta zartar da dokar kirkiro da masarautun gargajiya guda hudu bayan da dokar ta tsallake karatu na uku.

Wakilin mu na majalisa Abdullahi Isa ya rawaito cewar, a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis shugaban majalisar dokoki Abdul’aziz Garba gafasa ya sanar da hakan bayan tafka mahawara kan kudirin dokar.

A watan Mayun da ya gabata ne gwamnan jihar Kano ya  kirkiro da sababbin masarautu hudu a Kano, da nufin sake inganta ayyukan masarautu a jihar Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!