Labarai
Buhari yafi kowa sanin matsalar tattalin arzikin Najeriya -Sunusi Tambari Jaku
Babban mai bada shawara kan harkokin siyasa ga shugaban kasar Nijar Alhaji Sunusi Tambari Jaku ya ce shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari shi ne mafi sani gameda tsarin tattalin arzikin Najeriya domin kuwa mai daki shi ya san inda ke yi masa yoyo.
Tambari ya bayyana hakane lokacin da ya ke ganawa da wakilnmu Hassan Auwal Muhammad a kasar Nijar inda ya kara da cewa ko a baya ma gwammanatin Nigeria ta kulle iyakokinta bayan anyi yarjejeniyar (joint commission) wanda akayi a shekarar 1971 bayan tsarin yayi shekaru yana aiki.
“Shugaban kasar Najeriya shi ya san inda tattalin kasar sa ke da mastala kuma ya san yadda zai yi da tattalin kasar sa, haka zalika shi ne ya san abin da zai kasancewa kasar sa mafita” a cewar Sunusi Tambari.
Tambari ya ce ko da yake akwai yarjejeniya tsakanin kasasahen guda biyu to amma shin mutanen Nijar ne basu fahimci yadda yarjejeniyar take ba, ko kuma a yarjejeniyar babu batun rufe kan iyyakokin kasashen?, don ko a shekarar 1971 akwai yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen guda biyu na (joint commission), ga na Ecowas ga kuma (OMS wanda tsari ne da ya shafi kasuwanci tsakanin kasashen duniya) shin tsarukan ne basa aikin ko kuma rufe kan iyyakokin kasa ya girmi tsarukan.
Labarai masu Alaka:
Kowane Gauta: Yadda ziyarar shugaba Buhari ta kasance a Kano
Gwamnatin mu na kokarin inganta tsaro- Buhari