Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnatin mu na kokarin inganta tsaro- Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammad Buhari , ya jaddada kudirin gwamnatin sa na inganta tsaro ,tare da tattalin arziki na kasa ,da kuma yaki da cin hanci don bunkasa tare da cigaba kasar nan.

Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne a yau wajen bikin yaye mataimakan Sufurtandan ‘yansanda na kasa wato ASP karo na biyu, su 628 da akayi a jami’ar yansanda dake garin Wudil.

Shugaba  Buhari , ya kara da cewa kasancewar jami’an ‘yan sanda na daga cikin kashin bayan samar da tsaro a kasa, aikin samar da tsaro tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a ya ta’allaka ne kacokan kan Samar da kwararru kuma masu ilimi, da za su yi dai-dai da tsarin zamantakewar kasar nan mai al’umma daban -daban.

Shugaba Buhari ya bada umarnin tsas-tsaura matakan tsaro a jihar Borno

Shugaba Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaro su kara jajircewa akan aikin su

Shugaba Buhari zai gudanar da taro kan lamuran tsaro a fadar Asorok

A nashi jawabin, Kwamandan Makarantar , AIG Zanna Ibrahim,  ya ce duk da makarantar na fuskantar kalubale na dakunan dalibai da  Ajujuwan Karatu, da sauran wasu matsalolin hakan ba zai sa suti kasa a gwiwa ba wajen, samar da kwararrun ‘yan sandan da zasu yi kafada da kafada da takwarorin su na sauran kasashen duniya da suka cigaba.

Wakilin mu  na fadar gwamnatin jiha Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa daga cikin wadanda suka halarci wajen taron yayewar a  yau , akwai gwamnan jihar Kano , Dr Abdullahi Umar Ganduje, ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Mai Gari Dingyadi, ,shugaban hukumar lura da ‘yan sanda , Musiliu Smith, sai Babban Sufeton yan sanda na kasa ,  Muhammad Adamu, da sauran iyalai da abokanan arzikin wadanda aka yaye a yau.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!