Connect with us

Labaran Kano

Uwar jam’iyyar APC ta taya Ganduje murnar samun nasara a kotun koli

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa Adams Oshiomhole  ya taya gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje murnar samun nasara bayan da kotun koli ta tattabatar masa da nasarar da ya samu na zama gwamnan Kano.

A cewar Adams Oshiomhole wannan ‘yar manuniyace gwamnan Abdullahi Uamr Ganduje ya ci zabe babu wata tababa kasancewar jam’iyyar APC ita ce zabin Kanawa.

Kai tsaye : Kotun koli ta tattabar da Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Kai-tsaye : Yaushe ne za’a cigaba da sauraran shari’ar Ganduje da Abba?

Ko hukuncin Kotun Koli ya kawo karshen Siyasar Kwankwasiya a Kano?

Da dumi-dumin sa: Kotun koli ta tattabatar da nasarar da Ganduje ya yi

Adams Oshiomhole ya taya gwamnan murnar ne bayan daya  kai masa ziyarar don nuna Alhassan Ado Doguwa  a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tudunwada da Doguwa, wanda ya lashe zaben cike gurbi da kotu ta nemi a sake gudanar da shi da aka yi  a ranar Asabar din da ta gabata a gidan sa dake babban birnin tarayya Abuja

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Abba Anwar ya fitar cewa, Adams Oshiomhole yayi addu’ar fatan Allah ya karfafawa gwamnan gwiwa wajen gudanar da ayyaukan sa yadda ya kamata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!