Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai fara kwashe almajirai dake barace-barace akan tituna

Published

on

Gwamnatijn Jihar Kano zata fara kwashe almajirai da ke barace-barace a kan danjoji fadin jihar nan, baya ga bai wa alaranmomin wa’adin kwanaki Arba’in, da su maida almajiaransu mahaifarsu.

Kwamishiyar harkokin mata da kananan yara ta Jihar kano DR. Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayana hakan a yau, a wani taron manema labarai.

A cewar DR Zahr’u, daukan wannan mataki ya zama dole sakamakon bayanai sirri da gwamnati ke samu na yin lalata da wasu yara mata da ake zargin mabarata ne.

Ta kara da cewa, a bangaren kananan al’amajirai kuwa gwamnati ta bai wa alaranmomisu kwanaki Arba’in don mayar da su mahaifarsa.

Wakiliyarmu Yusuf Ali Abdullah ya ruwaito cewa, gwamnatin ba za ta saurarawa duk alaranmomin da suka bujirewa umarninta ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!