Labarai
Jiragen yaki za su iso Najeriya -Rundunar sojan sama
Rundunar sojan saman kasar nan zata karbi sabon jirgin shalkwafta da za’a yaki ‘yan ta’adda da shi kirar Mi-17IE ranar Alhamis 6 ga watan nan da muke ciki a dandalin Eagle dake babban birnin tarayya Abuja.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da daraktan yada labarai na rundunar Air Commodore Ibikule Daramola ya fitar a jiya Lahadi cewar, rundunar zata yi atisaye kafin da bayan karbar jirgin, kasancewar yana daya daga cikin horon sanin makamar aiki na sabon jirgin ga sojojin sama.
har ila yau, sanarwar ta ce za’a fara Atisayen ne daga yau Litinin 3 ga wata zuwa ranar Alhamis 6 ga wata.
A cewar sanarwar za’a gudanar da bikin ne cikin ‘yar kwarya kwarya ba tare an kashe wasu magundan kudade ba.
Zamfara:Jiragen yakin rundunar sojin sama sun fara luguden wuta
Rundunar sojin sama kasar nan ta tura jiragen yaki kirar jet guda 100 don bincike daliban Dapchi
Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen shalkwabta guda 2
Sanarwar ta kara da cewar, a don haka kada al’umma su firgota kasancewar za’a ga jiragen na shalkwata na shawagi a sararin sama.
Ka zalika idan za’a iya tunawa Najeriya ta karbi sabbin jiragin shalkwata guda 2 na yaki a ranar 29 ga watan Afirilun bara kafin bikin ranar ‘yan cin kai da aka yi a Abuja.