Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda wani Soja ya hallaka kansa da abokanan aikin sa

Published

on

Wani Sojan kasar nan dake cikin rundunar Operation LAFIYA DOLE da ke aikin samar da tsaro a Malam Fatori da ke jihar jihar Barno, ya kashe kansa da wasu abokanan aikin sa guda hudu.

Sannan Sojan ya jikkata wasu guda biyu, da yanzu haka ke cikin mawuyacin hali.

Kakakin rundunar sojin kasar nan, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana hakan, a wata takarda da ya fitar a yammacin jiya Laraba.

Zuwa yanzu haka dai ba a san dalilin da ya sanya sojan ya aikata hakan ba, amma a cewar Kanal Sagir Musa, suna nan suna bincike don gano abinda ya haifar da hakan.

Labarai masu alaka:

Jiragen yaki za su iso Najeriya -Rundunar sojan sama

Rundunar sojan sama ta lalata maboyar kungiyar ISWAP

Kanal Sagir Musa, ta cikin sanarwar ya ce, biyu daga cikin sojojin da sojan ya raunata suna karbar kulawa a Asibitin Sojoji dake Maiduguri.

Haka zalika, ya ce shirye-shirye sunyi nisa don mika gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu ga iyalansu domin yi musu jana iza.

Mai magana da yawun rundunar, ya kuma tabbatar da cewar za a kara tsaurara matakan tsaro don kare afkuwar hakan a nan gaba, tare da kira da jama’a da su kwantar da hankulan su don rundunar a shirye take da kare dukiyoyin su da rayukan su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!