Connect with us

Labarai

Rundunar sojan sama ta lalata maboyar kungiyar ISWAP

Published

on

Rundunar sojan saman kasar nan ta lalata maboyar kungiyar ISIS ta yammacin Afrika dake Arewacin  jihar Borno.

Babban daraktan yada labarai na rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar da ya fitar a yau a babban birnin tarayya Abuja.

Haka zalika rundunar ta kasha wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar a yankin Arrinna Ciki dake Tafkin Chadi.

Rundunar Sojan sama na Atisaye a Kano

Rundunar sojan Najeriya ta harbe yan bindiga 78 a watan jiya

Rundunar sojan kasar nan ta bukaci rufe offishin kungiyar Amnesty international

Air Commodore Ibikunle Daramola ya kara da cewar, rundunar ta gudnar da kai harin ne ta sama karkashin rundunar Operation LAFIYA DOLE.

A cewar sa babban daraktan yada labarai rundunar sojan saman ta aiwatar da aikin ne a tsakanin daya zuwa biyu ga watan Numban nan da muke ciki bayan ta samu bayanan sirrin dake nuna cewar ‘yan ta’adda na amfani da sansanin ne wajen kai hare-hare ga jami’an soja.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,906 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!