Connect with us

Labarai

Al’ummar Tudun Murtala sun koka

Published

on

Gidauniyar cigaban Al’ummar unguwar Tudun Murtala sun yi kira da gwamnatin jihar Kano da ta kawo musu dauki akan hanyar su ta Tudun Murtala sakamakon lalacewar da hanyar tayi.

Shugaban gidauniyar Alhaji Yahaya Bagobiri yace al’ummar suna fama da matsalar hanya da matsalar rashin magudanar ruwa data tashi daga unguwar Gwagwarwa zuwa Tudun Murtala dake karamar hukumar Nassarawa.

Alhaji Yahaya Bagobiri ya bayyana hakan ne a ya yin taron da gidauniyar ta shirya don taya murna ga Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan na jami’ar Al’qalam bisa zama Farfesa da yayi.

Labarai masu alaka:

Wasu ‘yan kasuwar Sabon gari sun koka kan yunkurin Uba Zubairu

Inda Ranka: ‘Yan kasuwa sun koka kan biyan harajin wuta mai hasken rana a Kano

Ya ce Sheikh Abdullah Saleh Pakistan ya dade yana bada gudunmuwar ilimin addinin Islama dana zamani a unguwar Tudun Murtala wanda hakan yasa al’ummar unguwar ba zasu taba mantawa da shi ba.

Da yake nasa jawabin a yayin taron Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan bayyana farin cikin sa ya yi  bisa karramawar da jami’ar Al’qalam tayi masa da gidauniyar unguwar Tudun Murtala da sauran al’ummar unguwar baki daya.

Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa al’ummar unguwar sun kira ga masu kudin unguwar da su yi koyi da Sheikh Pakistan kan irin abin da yake yiwa al’ummarsa.

Labarai

Amaechi ya karya ta labarin ya tsallake rijiyar da baya

Published

on

Ministan sufurin Rotimi Amechi ya karyata labarin da ake yadawa cewa ya tsallake rijiya da baya, bayan da masu satar mutane suka kaiwa jirgin kasa hari a Mando dake jihar Kaduna, da yammacin jiya Lahadi.

Rotimi Amechi ya wallafa hakan a shafin sa na Twitter cewa labarin karya ce tsagwaran ta, a don haka al’umma su yi watsi shi.

Rahotanni sun bayyana cewar, a jiya Lahadi ne masu satar mutane suka yi artabu da jami’an tsaro dai-dai lokacin da fasinjoji za su sauka a tashar jirgin kasa dake Rigasa.

Sai dai da safiyar yau ministan ya karya ta cewa yana cikin jirgin dai-dai lokacin da aka kai harin.

Wata majiya mai karfi daga tashar jirgin kasan ta Kaduna ta tabbatarwa da Freedom Radio afkuwar harin, amma bayan da ministan sufurin ya sauka daga jirgin kasar ne.

Labarai masu alaka:

Kotu tayi watsi da bukatar soke sabbin masarautu

Muhimman abubuwan dake faruwa yanzu haka a Kannywood

Continue Reading

Labarai

Kotu tayi watsi da bukatar soke sabbin masarautu

Published

on

Babbar kotun jihar Kano ta kori karar da masu zabar sarki na masarautar Kano suka shigar suna kalubalantar kirkirar sabbin  masarautu guda hudu da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Da yake yanke hukunci a safiyar yau litinin, mai shari’a Ahmed Tijjani Badamasi ya kara tabbatar da hukuncin da mai shari’a Usman Na’aba ya yi a ranar 21 ga  watan Nuwamban shekarar da ta gabata na tabbatar da masarautun.

Majalisar dokoki ta Kano ta amince da dokar kafa masarautu 4

Ganduje ya sakawa dokar kikiro masarautu hannu

Kotu ta dage sauraran karar dattawan Kano kan sabbin masarautu

 

Idan za’a iya tunawa masu nada sarki a masarautar Kano wanda suka hada da Madakin Kano Hakimin Dawakin Tofa Yusuf Nabahani , da Makaman Kano kuma hakimin Wudil Abdullahi Sarki-Ibrahim da sarkin Dawaki Mai Tuta kuma hakimin Gabasawa Bello Abubakar da sarkin ban Kano hakimin Dambatta Muktar Adnan sune suka shigar da karar suna kalubalantar kirkirar sabbin masarautun.

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Jami’an tsaro ku kama duk mai tunzura jama’a-Sarkin musulmi

Published

on

Sarkin Musulmi

Shugaban majalisar koli ta addinin musulunci kuma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci jami’an tsaron  kasar nan da su dauki matakin kama duk wami malamin addini da ke yada kalaman tunzura jama’a.

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana hakan ne yayin wani taron zaman lafiya da kuma gina kasa, da majalisar Da’awah ta kasa ta shirya a garin Jos babban birnin jihar Plateau.

Ya ce, akwai bukatar a rika gudanar da harkokin addinai ta yadda za a kaucewa tada rikice-rikice.

Matsalolin aure: Sarkin Kano ya bukaci a koma makaranta

Abinda ya sa ban ce komai ba kan batun sanya Hijab a Jamia: Sarkin Musulmi

Sarkin musulmi ya bukaci gwamnatin tarayya ta zage dantse don magance matsalolin tsaro

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya kuma yi kira ga kungiyar Jama’atu Nasril Islam da kungiyar Kiristoci ta kasa CAN da su yi dukkan mai yiwuwa wajen kawo karshen cece-kucen dake faruwa tsakanin mabiya addinan biyu a kafafen yada labarai.

 

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!