Labaran Wasanni
Madrid na fuskantar barazanar ficewa daga Champions League
Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester City, ta kama hanyar tsallakawa zuwa zagayen dab dana kusa dana karshe wato Quarter final a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, bayan da ta je har gida ta casa Real Madrid, da ci 2-1, a wasan farko na zagayen siri daya kwale wanda aka fafata a filin wasa na Santiago Bernabeu.
Dan wasan Real Madrid, Isco Alarcon, ne ya fara zura Kwallo a ragar Manchester City, a minti 60, bayan dawowa hutun hutun rabin lokaci da taimakon dan wasa Vinicius Junior, sai dai a minti na 78 Manchester City, ta biya bashin Kwallon bayan da dan wasanta Gabriel Jesus, ya zura Kwallo a minti na 78 a ragar Real Madrid.
A minti 83 na wasan, dan wasan Manchester City Kevin De Bruyne, ya zura Kwallo ta biyu da bugun daga mai sai mai tsaron gida wato Penalty bayan da dan wasan bayan Real Madrid Dani Carvajal ya yi keta a ciki yadi na 18, ga dan wasan Manchester City Raheem Sterling.
Madrid ta kara samun koma baya, inda ana dab da za’a tashi kyaftin din kungiyar Sergio Ramos, ya karbi katin kora wato jan kati, bayan da ya yi keta ga dan wasa Gabriel Jesus na Manchester City, Wanda hakan ya sa ba zai buga wasa na biyu ba tsakanin kungiyoyin nan da makwanni uku masu zuwa.
You must be logged in to post a comment Login