Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Lyon ta bawa duniya kwallo mamaki

Published

on

Kungiyar Kwallon kafa ta Lyon dake kasar Faransa, ta bada mamaki ga duniyar Kwallo inda ta samu galaba a kan kungiyar Juventus daga kasar Italiya, a wasan farko na zagayen siri daya kwale na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a wasan da aka fafata a filin wasa na Groupama Stadium dake kasar Faransa.

Dan wasa Lucas Toussart, wanda ya zo a matsayin aro daga kungiyar Hertha Berlin, ne ya zura Kwallo daya tilo a minti na 31, da take wasa bayan samun taimako daga hannun Houssem Aouar.

‘Yan kallo Dubu 57, da 335 suka kalli wannan wasa, wanda alkalin wasa Jesus Gil, daga kasar Andalus wato Spaniya ya busa.

Yanzu haka dai, kungiyon biyu na dakon karawar su ta biyu, wadda zata tabbatar da waye zai shiga zuwa zagaye na gaba filin wasa na Juventus Stadium, dake birin Turin na kasar Italia.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!