Labarai
An gurfanar da tsohon kwamishinan Lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf gaban babbar kotun Kano
A yau Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da tsohon kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, gaban wata babbar kotun jihar bisa zargin sa da yin sama da fadi da kudi dala dubu 294 da.
Adadin kudin wanda kimar su dai-dai da Naira miliyan 47 da dubu 168, kudi ne da aka baiwa tsohon kwamishinan don biyan alawus-alawus da kuma sauran bukatu na daliban jihar Kano a Cairo ta kasar Masar.
Kotun karkashin mai shari’a A’isha Danlami Rabi’u ta bayanr da belin tsohon kwamishinan kan Naira dubu 200.