Labaran Kano
A daina siyasar uban gida a Najeriya domin cigaban demokradiyya -Farfesa Kamilu
Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce matukar ana so a karfafa tsarin dimukuradiyyar kasar nan ya zama wajibi a rika baiwa mutane wadanda suka zaba ba wai a rika yiwa jama’a karfa-karfa ba kamar yadda kotunan dauka kara ke yi a yanzu.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana haka ne ta cikin shirin muleka mu gano na gidan rediyo Freedom na musamman a jiya Lahadi da ya mayar da hankali kan daukaka kara na zubaka a fadin kasar nan.
Kamilu Sani Fagge ya kara da cewa irin wannan hali na kwace nasara daga wajen wanda yayi nasara ko wanda jama’a ba shi suke so ba yana haifarda mummunan tashin hankali dama sanya fadace fadace a tsakanin jama’a.
Masanin kimiyyar Malam Kamilu Sani Fagge ya ce matukar anaso a kawo gyara a siyasar cikin gida dole ne a rika baiwa mutane wanda suka zaba domin ta haka ne kawai za’a kawo gyara a cikin siyasar cikin gida bawai a kakabawa mutane wanda ba shine zabin su ba domin hakan tamkar hawan kawara ake yiwa doka.
Ya kara da cewa matsalar siyasar wannan zamani babu akida a cikinta ko kadan asalima ‘yan siyasa sun mayar da siyasa ne tamkar kasuwa da zasu zuba jari domin samun riba amma badan su ciyar da jama’a gaba suke ba ,sai don biyan bukatunsu na kashin kai.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa daya bibiyi yadda shirin ya wakana ya ruwaito farfesa Kamilu Fagge na cewa matukar ana so a kawo gyara dole ne a yiwa tsarin yadda ake gudanar da harkokin siyasa a fadin kasar nan.