Labaran Kano
Kananan hukumomi su dinga kasafin kudin su da kan su- Abdulrrazak Alkali
Kungiyar dake karfafawa al’umma wajen shiga Demokradiyya a dama da su wato ‘’organization for community civil engagement’’ ta ja hankalin gwamnatocin kasar nan da su bar majalisun dokokin jihohin su, su dinga gudanar da kasafin kudin su da kan su kamar yadda tsarin mulkin kasa ya basu dama.
Shugaban kungiyar Abdulrrazak Alkali ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kan jama’a da kungiyar ta gudanar hadin gwiwa da hukumar raya kasashen Burtaniya DFID kan wayar da kan jama’a ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasa ya baiwa ‘yan majalisu wajen gudanar da aikin su batare da sa hannun gwamnatocin Jihohin su ba.
Abdurrazak Alkali ya kuma ce, baiwa ‘yan majalisu damar kashe kudaden su shine zaisa a samu cikakkaen shugabanci na gari a majisun ba tare da sun zama ‘yan amshin shatan gwamnatocin ba.
Da yake nasa jawabi yayin taron shugaban hukumar raya kasashen Burtani DFID Jibril Giginyu cewa yai, samun damar baiwa majalisun damar cin gashin kan su zai baiwa majalisun damar gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.
Wasu daga cikin mutanan da suka halarci taron sun bayyana ra’ayoyin su kamar haka.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya ruwaito cewa yayin taron malamai da dai dai kun jama’a sun gudanar da jawabai game da muhimmancin baiwa majalisun jihohi damar cin gashin kansu.