Addini
A fara duban watan Sha’aban – Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya umarci Musulmai a faɗin ƙasar nan da su fara duban watan Sha’aban 1443AH da ga yau Alhamis.
Watan Sha’aban shi ne na takwas a jerin watannin Musulunci, wanda da ga shi sai watan Ramadan.
Sultan ya bada umarnin ne a wata sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu, Shugaban Kwamitin Shawarwari na Harkokin Addini na Masarautar Sokoto, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
Ya ce a na sanar da al’ummar Musulmi cewa Alhamis, 29 ga watan Rajab, wacce ta zo daidai da 3 ga watan Fabrairu, ita ce ranar da za a fara duban jaririn watan Sha’aban 1443 AH.
“Sabo da haka sai Musulmai su fara duban jaririn watan Sha’aban a yau kuma duk wanda ya gan shi ya kai rahoton zuwa ga Hakimin ko dagaci ko mai unguwa mafi kusa domin ƙarin bayani,”in ji Sultan.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya taimaki al’ummar Musulmi a kan yi wa addini hidima.
You must be logged in to post a comment Login