Labaran Kano
A gaggauce: Ganduje ya bai wa mai buƙata ta musamman takardar ɗaukan aiki
Gwamnatin jihar Kano ta bai wa wani Malami mai lalurar gani takardar ɗauka aiki kai tsaye.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bai wa ma’aikatar ilimi ta jihar umarnin miƙa takardar ɗaukan aiki ga malamin.
Da yake bayyana amincewar sa da bada takardar ɗaukan aikin, gwamna Ganduje ya ce “A ƙoƙarina na inganta rayuwar al’umma, a madadin gwamnatin Kano na amince a baka takardar ɗaukan aiki ɓangaren koyarwa kai tsaye”.
Gwamnan ya bai wa Kwamishinan ilimi Muhammad Sanusi Sa’idu Ƙiru umarnin tura Dahuru Abdulhamid Idris zuwa makarantar masu buƙata ta musamman ta Tudun maliki domin ya ci gaba da koyarwa.
Tun da fari dai Malamin mai suna Dahuru Abdulhamid Idris na yin koyarwa ta sa kai wato Voluntery gabanin ba shi takardar ɗaukan aikin.
Wannan dai na cikin sanarwar da sakataren ƴaɗa labarai na gwamnan Abba Anwar ya fitar.
You must be logged in to post a comment Login