Labaran Kano
A haramta shigo da tufafi Najeriya na tsawon shekara 5: Majalisar dattijai
Majalisar dattijai a zaman ta na jiya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta haramta shigo da kayayyakin sutura daga kasashen waje na tsawon shekaru biyar domin baiwa masana’antun da suke sarrafa kayan sutura na cikin gida damar bunkasa.
Wannan mahawarra ta biyo bayan wani kudiri da sanata Kabir Barkiya na jamiyya APC a mazabar Katsina ta tsakiya ya fitar, a yayin tattaunawa da ‘yan majalisar.
Ya ce akwai bukatar tabbatar da hakan da gaggawa don inganta harkokin sarrafa kayayyakin sutura a Najeriya.
Majalisar dai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da kayan aikin da ya kamata domin tabbatar da yiwuwar hakan, musamman ma wutar lantarki wanda shine zai taimakawa masana’antun cikin gida su habbaka.
‘Yan Majalisar dai sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mara wa masu kananan masana’antu wajen basu rance na kudi, su kuma saukaka musu karbar rancen domin inganta harkokinsu a bankunan masana’antu.
Barkiya ya kara da cewar masana’antu na da matukar muhimmanci wajen cigaban tattalin arzikin kasa.
Sanata Ahmad Lawan ya musanta zargin jagorantar gyara ga kundin tsarin mulkin kasa
Wanda a shekarun baya a 1960 zuwa 1970 suna daga cikin abubuwan da suka inganta tattalin arzikin Najeriya, inda ake da kamfanoni sama da 140.
Ya ce a shekara ta 1991 masana’antun Najeriya sai da suka samar da kudaden shiga da adadin su ya kai kaso 67 cikin dari ,inda hakan ya samar da ayyukan yi da kimanin kaso 25 cikin dari a fannin kamfanoni dake samar da kayayyakin da suka danganci tufa.
Sanata Barkiya ya bayyana masana’antun da cewa sun fuskanci koma baya ne a shekaru 20 da suka wuce, inda da dama daga cikin kamfanonin da ke saraffa tufa musammam na jihohin Kano da Kaduna da ma na Aba suka durkushe sakamakon rashin basu muhimmanci da Najeriya ke yi da matsalolin shigo da kaya daga kasashen wajen.
Da yake mara masa baya sanata Robert Boroffice na jam’iyyar APC da ke wakiltar Arewacin jihar Ondo ya ce shigo da kayayyaki daga wasu kasashen shine ummul abasin dakushewar masana’antu a Najeriya
Inda ya ce rufe iyakokin Najeriya da aka yi a wannan lokaci shi ne kadai hanyar da za’a bi wajen dawo da martabar kasar nan, tare da nuni da yadda kasar Sin ta samu cigaba ta hanyar rufe iyakokin ta har na tsawon shekaru 40, da yin haka kuwa kasar ta samu cigaban da duniya ke gani a yanzu haka.
A cewarsa rufe iyakokin Najeriya ne kadai hanyar da za’a dawo da martabar masana’antun mu da kuma baiwa yan kasa karsashin amfani da kayan da aka saraffa su a gida.
Shima shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya ce a yanzu da Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen Afrika ya zama wajibi wajen tabbatar da hana shigo da sutura daga waje.