Connect with us

Labarai

A hukunta masu hannu a gobarar ofishin Akanta na kasa-Joe Odumakin

Published

on

Shugabar  cibiyar kawo Canji, wato  ‘center for change’ Dakta, Joe Okei- Odumakin,  ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gufanar da wadanda aka kama suna da hannu wajen gobarar da ta tashi a ofishin Akanta  Janar na kasa.

Dakta , Joe Okel Odumakin ta bukaci hakan ne ta cikin sanararwar  da ta fitar a birnin Lagos, in da tace ya zama wajibi a kama tare da gurfanar da wadanda suka haddasa gobarar.

Labarai masu alaka.

A Yanzu -Yanzu : gobara ta tashi a Ofishin akanta na kasa

Gobara ta lalata dukiyoyi masu yawa a Kano

Kazalika Odumakin ta nemi Gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike don gano musababin gobarar.

Har ila yau shugabar cibiyar  ta ce kada Gwamnatin tarayya ta kyale batun gobarar ya tafi ba tare da an hukunta masu hannu a cikin laifin tashin ta ba.

A jiya Laraba  gobarar ta tashi a ofishin Babban Akanta na kasa, wanda kawo yanzu haka  ba’a san abinda ya haddasa ta ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!