Connect with us

Kiwon Lafiya

Covid 19: Gwamnatoci su kara kokari-Dakta Muhammad Abdu

Published

on

Wani likitan Dabbobi Dakta Muhd Abdu, yace cutar Corona ta hana masu kiwo sakewa wajen nemo abincin dabbobi harma da masu sana’ar noma da da sauransu.

Muhammad Abdu ya bayyana haka ne ta cikin shirin Duniyar mu a yau na nan Freedom Rediyo

Likitan yace gwamnati na  da rawar da zata taka wajen taimakawa al’ummar kasar nan musamman  tallafin  kayan abinci da kayan noma da makamantan su.

Labarai masu alaka.

Wasu ‘yan Najeriya sun kamu da cutar COVID-19 a kasar Sin

Killace kai da hana Sallah a cikin jama’a lokacin Annoba dai -dai ne a Musulunci

A nasa jawabin  Alhaji Abdulkadir Mustapha,  wanda ya kasance  cikin shirin kuma babban manomi a nan jihar Kano yace noma a kasar nan yaja baya ba kamar  lokacin baya  ba da kayan abinci suka wadata, sai dai  yanzu kayan basa siyuwa a kasuwanni sabo da bullar cutar ta covid 19

Bakin sunyi kira da Gwamnato ci a dukkan matakai dasu maida hankali wajen yakar cutar don samun kwanciyar hanakali tare da dawowa harkoki kamar yau da kullum.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!