Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ronaldinho ya shaki iskar ‘yanci

Published

on

Bayan shafe kwanaki talatin da biyu a cikin Kurkuku , a kasar Paraguay tsohon gwarzon dan wasan duniya karo  biyu dan kasar Brazil Ronaldinho,  da dan uwansa Roberto de Assis , sun shaki iskar ‘yanci bayan da Alkali Gustavo Amarilla ya bada belin su akan kudi sama da  Fam miliyan daya.

An dai kama tsohon dan wasan  na Barcelona ne a farkon watan Maris, shi da dan uwan sa bisa zargin shiga kasar Paraguay da fasfon Bogi , sai dai bayar da belin nasu, yanzu an sake su tare da yi musu daurin talala a gida har zuwa lokacin da za’a kammala bincike.

Jim kadan bayan shigar su kasar ta Paraguay  a baya, hukumomin kasar suka damke su bisa zargin fasfon, tare da tisa keyar su zuwa gidan kaso na Agrupacion Especializada , bayan kama su da akayi a wajen shakatawa na’ Resort Yacht and Golf Club Paraguay’.

Labarai masu alaka.

Hanyar da Diago Simeone ya bi wajen fitar da Liverpool a Champion

‘Yan wasa na bada gudunmowa don yakar Corona Virus

 

A lokacin da yana gidan Kason, hotuna daban -daban hade da bidiyon dan wasan sun yadu a shafukan sadarwa na Zamani, da yake Kwallo da aiyyukan nishadantar da jama’a a gidan kason.

Sai dai duk da haka, Ronaldinho da dan uwansa sun musanta aikata ba dai -dai ba , inda yace fasfon dan kasuwar kasar Brazil Wilmondes Sousa Liria, ne ya basu shi kyauta don haka basu da masaniyar cewar na bogi ne.

Sai dai a bayyane yake  dan wasan bai ji dadin abinda ya faru ba ,kamar yadda tsohon dan wasan kasar Paraguay , Nelson Cuevas ya bayyana wa gidan Rediyon CNN, “Kowa ya san shi da nishadi da murmushi amma yanzu haka dana ke muku magana dana je gaisawa da duba Abokina murmushin sa yayi kaura  sakamakon yana wajen da bai saba dashi ba “.

Tsohon dan wasan Paris Saint Germain, Barcelona da Ac Milan, Ronaldinho ya wakilci kasar sa ta Brazil har sau 97 inda yq zura Kwallo 33, daga shekarun 1999 zuwa 2013, yana kuma daga cikin jiga jigan ‘yan wasan da suka daukar wa kasar Kofin duniya na shekara ta 2002.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!