Labarai
A karo na biyu lauyan Ibrahim Magu ya aike wa kwamitin bincike wasika
A karo na biyu lauyan dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasha ta EFCC, Wahab Shittu ya rubuta wasika ga shugaban kwamitin da ke binciken tsohon shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu a kan ya basu damar daukar bidiyon yanda binciken yake gudana.
Wahab Shittu ya bukaci shugaban kwamitin Ayo Salami da ya bayar da Tsofaffin kwafin bidiyon da aka fara dauka tun farkon binciken domin nuna shi ga masoyan sa kafin daukar mataki na gaba.
Ta cikin wasikar Lauyan Ibrahim magu ya ce yin hakan bai sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan ba karkashin sashi na talatin da shida ba.
A cewar Wahab Shittu kamata yayi kwamitin ya ware rana guda don baiwa Daktacen shugaban hukumar ta EFCC damar kare kansa a gaban Jama’a domin suma su san halin da ake ciki.
A dai ranar Shida ga watan yuli ne Jami’an tsaro suka cafke dakatatten shugaban hukumar ta EFCC a gaban Offishinsa dake Abuja.
You must be logged in to post a comment Login