Coronavirus
A karon farko Lagos zata bude wuraren ibadu tun bayan bullar Corona
Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo Olu ya ce za a bude wuraren ibadu na jihar, a ranar bakwai ga watan agustan da muke ciki.
Babajide na bayyana hakan ne lokacin da ya ke zantawa da kwamitin kar ta kwana na yaki da cutar covid-19 a yammacin yau.
Ya ce, tun a watan Maris din shekarar da muke ciki ne gwamnatin jihar ta yanke hukuncin rufe guraren ibadu don dakile yaduwar cutar ga al’ummar.
Idan dai za a iya tunawa tun a watan Yunin da ya gabata ne kwamitin yaki da cutar corona na gwamnatin tarayya ya amince da bude guraren ibadu a kasar, sai dai gwamnatin jihar Lagos ba ta bude ba kamar yadda aka bada umarni.
Cikin hukuncin da Babajide ya yanke din a yau, ya ce a kowanne gurin ibada baza’a wuce kaso hamsin na masu ibada ba, inda gwamnatin zata sanya idanu na wasu makwanni don tabbatar da an bi dokar da ta gindaya.
Jihar lagos dai ita ce kan gaba a cikin jihohin kasar nan da ta ke samun mafi yawan adadi na masu cutar corona, inda adadin wadanda suka kamu da Cutar ya kai dubu 15, 000 sai wadamnda suka rasa rayukan su sandaiyyar cutar ya kai dari 200.
You must be logged in to post a comment Login