Labarai
A kwai hukumomi 65 da ba’a taɓa tantance su ba- majalisar wakilai
kwamitin sanya idanu kan harkokin kuɗi na majalisar wakilai ya ce akwai hukumomin gwamnati 65 da ba a taɓa tantance su ba tun lokacin da aka ƙirƙiro su.
Shugaban kwamitin Oluwole Oke ne ya bayyana hakan yayin bude babban taron binciken hukumomin gwamnati kan sha’anin kudi.
Oluwole Oke ya ce, ma’aikatu 12 da wasu sashi na wasu daga cikin ma’aikatu 65 ba a taɓa bincikar su ba, tun daga shekarar 1993 zuwa 2010.
A cewar sa, ma’aikatun gwamnati 76 sun gaza gabatar da rahotannin su ga ofishin akanta na tarayya a shekarar 2011, yayin da ma’aikatu 85 suka gaza gabatar da nasu a shekarar 2012, sai guda 109 da ba su shigar da nasu ba a 2013.
Sauran 148 ba su ba da rahotannin su ba a 2014 sai 215 s…
You must be logged in to post a comment Login