Addini
A samar da kotun hukunta masu laifin cin hanci – MURIC
Kungiyar dake rajin kare hakkin musulmi ta (MURIC) ta bukaci da a samar da kotu ta musamman da zata rika shari’ar ayyukan da suka shafi cin hanci da rashawa da masu fyade a kasar nan.
Daraktan kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a yau ta cikin wata sanarwar da ya fitar a Abuja.
Ya ce, kiran nasu ya zama wajibi duba da yadda ayyuakan cin hanci da rashawa ke lalata zaman lafiya da ci gaban kasa har ma da tabarbareawr tsaro.
Akintola ta cikin sanarawar ya bayyana cewa, dole ne a yaki ayyukan cin hanci da rashawar a kasar nan sakamkon yadda laifukan ke kara yawa da rashin kaddamar da hukunci akan wanda aka kama da laifi a kotunan kasar nan.
Sanarwar ta kuma ce, akwai laifuka da yawa na cin hanci da rashawa da ayyauka fyade har ma da amsu garkuwa da mutane a kotuna wanda har yanzu aka gaza yanke hukunci a kan su, yayin da wasu ke fakewa da sashin shar’ar musulunci don tserewa daga tuhumar da ake yi musu.
Akintola ya c samar da kotun ita ce hanya mafi sauki da za a rika hukunta masu ayyukan cin hanci da rashawa akan lokaci inda ya buaci majalisar jihar Kano da ta amince da kudirin don samar da mafita.
You must be logged in to post a comment Login