Connect with us

Kiwon Lafiya

A sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe 8na dare zuwa 6 na safe a jihar Borno

Published

on

Gwamnatin jihar Borno ta sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na safe a birnin Maidugurin jihar, sabanin da da yake karfe 10 na dare zuwa shida na safe.

Kwamishinan yada labaran jihar Dakta Muhammad Bulama ne ya bayyana hakan, lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri.

Bulama yace dokar hana zirga-zirgar na dan wani lokacin ne, wato daga ranar 2 zuwa 6 ga watan da muke ciki na Janairu, kuma anyi hakan ne da nufin kara inganta tsaro a yankin.

Yace gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirgar ne sakamakon shawarar hakan da ta samu daga rundunar Operation Lafiya Dole.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!