Labarai
A wata mai kamawa sabuwar makarantar koyar da zamantakewar aure za ta fara aiki a Kano-Ibn Sina

Hukumar HISBAH ta jihar Kano ta ce, a wata mai kamawa ne sabuwar makarantarta ta koyar da zamantakewar aure za ta fara aiki.
Babban Kwamandan hukumar Malam Muhammad Haruna Ibn Sina ne ya bayyana hakan a wata zantawa da Freedom Radio.
Ibn Sina ya ce, a matakin farko zaɓi ne ga wanda ke da sha’awa, amma a nan gaba za su yi ƙoƙarin ganin an mayar da shi doka ga duk mai son yin aure a Kano.
You must be logged in to post a comment Login