Labarai
Yau ake sa ran kotu za ta yake wa Ekweremadu da matarsa hukunci
A yau ne Juma’a ne kotun hukunta manyan laifuka ta Old Bailey da ke Birtaniya za ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar nan Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice Ekweremadu da wani likita hukunci.
Wannan dai ya biyo bayan samun ɗan majalisar dattijan tare da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan-adam.
Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo wani mutum saboda a cire masa koda, inda ake sa ran yanke musu hukunci a karon farko a irin dokokin bauta ta zamani.
Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, ya kasance mai gudanar da wata ƙaramar sana’a a jihar Legas, ina aka kai shi Birtaniya a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke birnin London.
Sai dai ya ce, an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, daga baya ne ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya.
You must be logged in to post a comment Login