Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ilimi ya samu tasgaro a Kano- Dakta Kabiru Sufi

Published

on

Wani masanin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga jami’a a Kano CAS, Dakta Kabiru Sufi Sa’id, ya ce harkar ilimi a jiar Kano ta samu koma baya musaman a matakin Firamare.

Dakta Kabiru Sufi Sa’id, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakiliyar Freedom Radio Hafsat Abdullahi Danladi, da safiyar yau Juma’a.

Tattaunawar tasu dai, ta mayar da hankali ne kan kalubalen da matasa ke fuskanta a wannan lokaci.

Ya kuma ce, kamata ya yi gwamnati mai jiran gado ta yi duba na tsanaki kan harka ilimi da kuma samar wa da matasa ayyukan yi.

Haka kuma ya bayyana rashin samun ingantacce ilimi a matsayin abinda ke kara ta’azzara matsalolin kwacen wayoyin mutane da bata gari ke yi da kuma fashin daji da ake fuskanta har ma da garkuwa da mutane da aikata muggan laifuka.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!