Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A yau ne majalisar dattijai zata tabbatar sunayen ministoci bayan tantance su

Published

on

A yau talata ne majalisar dattijan kasar nan za ta tabbatar da mutanen da shugaban kasa ya tura ma ta a matsayin ministocin da yake nadawa bayan ta kammala tantance su.

Daga larabar makon jiya zuwa jiya litinin, majalisar ta tantance sunayen mutane 39 daga cikin 43 da shugaba Buhari ya tura mata don nada su ministocin.

Wadanda aka tantance jiyan sun hadar da tsohon ministan lantarki ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola daga Jihar Lagos, da Gbemisola Saraki daga Kwara, sai Sulaiman Adamu daga Jigawa.

Sauran su ne Maryam Katagum daga Bauchi da Goddy Jedy-Agba daga Cross River da Clement Agba dag Edo da tsohon ministan harkokin wajen kasar nan Geoffrey Onyeama da tsoon gwamnan Osun Ra’uf Aregbesola da kuma Muhammad Mahmoud daga Jihar Kaduna.

Wadanda za tantance a yau din su ne Sabo Nanono daga nan Kano da tsohon ministan yada labarai Lai Muhammad daga Kwara da kuma Saleh Mamman daga Jihar Taraba.

To sai dai jam’iyyar PDP ta yi kira ga majalisar dattijan ta mika sunayen mutanen ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ksa EFCC don sake tantance su sosai, kasancewar ana zargin wasu tsoffin gwamnoni da ministoci da almudahana iri-iri.

Wannan na kushe cikin wata sanarwa mai kunshe da sa hannun sakataren yada labaran PDP na kasa Kola Ologbondiyan.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!