Labarai
Abdullahi Abbas ne halastaccen shugaban jam’iyya a Kano – APC
Jam’iyyar APC ta ƙasa ta goyi bayan Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar Kano.
Daraktan yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Alhaji Salisu Na’inna Ɗanbatta ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.
Ɗanbatta ya ce, tsarin jam’iyyar shi ne duk inda ta ke da Gwamna to shi ne jagoran jam’iyya.
Saboda haka duk inda aka yi zaɓe saɓanin wannan to ba halastacce bane, kuma ya saɓa da tsarin jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa “Gwamna ko mai babban muƙami idan bamu da Gwamna a jiha shi ne gaba a jam’iyya, a duba a gani wane zaɓe ne aka yi a inda hukumar zaɓe ta turo wakilai?”.
“Wane zaɓe ne jami’an tsaro suka je suka tabbatar da tsaro a wajen? Wannan shi ne sahihin zaɓen da muka sani”.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan zaɓen shugabannin jam’iyyar na jihohi wanda ya bar baya da ƙura a wasu yankunan.
An samu rabuwar kai a jihohin Neja da Kwara da Legas da kuma jihar Ogun da sauransu.
A nan Kano ma tsagin Gwamna Ganduje ya gudanar da zaɓensa tare da ayyana Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin wanda ya yi nasara.
A ɗaya ɓangaren shi ma tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya jagoranci nasa wanda ya ayyana Alhaji Ahmadu Haruna Ɗanzago a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.
You must be logged in to post a comment Login