Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

An Tashi Lafiya

Abin da taron matan shugabannin Afrika zai mayar da hankali a Abuja

Published

on

A ranar Litinin din nan ne ake shirin fara babban taron ƙungiyar samar da zaman lafiya ta matan shugabannin ƙasashen Afrika wato African First Lady Peace Mission karo na 9.

A wannan karon dai Najeriya ce ke karɓar baƙuncinsa, wanda kuma tuni aka ɗauki harama, inda matan shugabannin ƙasashen Afrika da dama suka hallara a babban birnin tarayya Abuja.

Mai dakin ta shugaban kasa Hajiya Aishatu Buhari wadda ta karbi bakwancin taron kungiyar samar da zaman lafiya ta matayen shugabannin kasashen Afrika, tace sun shirya taron ne domin kara dabbaka manufarsu ta tabbatarda zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen yanken Afrika baki daya.

Ta kara da cewa shirin da kungiyar ta yi ne na wadannan shekaru ya sanya su tunanin sake farfado da tafiyar tasu domin su ci gaba da bada tasu gudunmawar a matsayin su na Iyaye wajen tabbatarda zaman lafiya a tsakanin kasashen.

A nata bangaren mai dakin shugaban kasar Burundi Madam Angeline cewa ta yi tazo Najeriya ne domin ta mika sakon godiyar al’ummar kasar Burundi ga gwamnatin Najeriya musamman a wannan taro.

Ita dai wannan kungiyar an kirkireta ne a shekarar 1997 domin ta kara hada kan kungiyoyin matayen shuwagabannin kasashen Afrika da nufin kawo karshen matsalolin yake – yaken dake faruwa a tsakaninsu da kuma nusar da kasashen illar da hakan ke da shi.

Taron dai wanda ake saran halartar matayan shuwagabannin kasashen Ghana , Cote D’voire , Jamhuriyar demokradiyyar Congo, Laberia, Niger , Murtania , Sierra Leone da kuma Nimibia da sauran wasu kasashen na Afrika.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!