Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An tsinci gawar wata mata da aka daddatsata a wani kango a Kano

Published

on

Al’ummar yankin Guringawa a ƙaramar hukumar kumbotso anan Kano sun wayi gari da ganin gawar wata mata a cikin kango.

Tun da fari dai wasu yara ne da ke ƙoƙarin gaurawa cikin kangon suka lura da wani buhu na malalar da jini.

Daga nan ne sai yaran suka fara ihu tare da neman agajin al’umma kan su zo su ga wannan lamari.

Ko da zuwan al’ummar kuwa, sai suka tarar da gawar wata mata da aka daddatsata gunduwa-gunduwa kuma aka nannaɗe a buhu tare da jefata a kangon.

Ɗaya daga cikin matan da ke maƙwabtaka da kangon wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce, ba tun yanzu ba suke fuskantar barazana a cikin kangon ta hanyar yasar da gawa da kuma shaye-shaye da zubar da bola.

Alhaji Ghali Sulaiman shi ne dagacin yankin Guringawa ya tabbbtar da faruwar lamarin, har ma ya yi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankalin su saboda hukuma za ta shiga cikin lamarin.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce za su faɗaɗa bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!